Kuraye sun cinye wani mutum a Kenya

Ana tsammanin Kuraye sun kashe wani mutum tare da cinye kusan dukkan naman jikinsa a kasar Kenya.
Shugaban gundumar da abin ya faru Cif Vincent Leipa, ya sanarwa da al'ummarsa cewa wannan ne karo na biyu da irin wannan ta taba faruwa a wannan yanki da ke garin Ongata Rongai.
Al'amarin ya faru ne ranar Juma'a da daddare a lokacin da mutumin ke kan hanyar komawa gidansa a garin wanda ke kusa da gandun namun daji na Nairobi babban birnin kasar.
- <link type="page"><caption> Kura ta ciji wani yaro a Afirka ta kudu</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/news/2016/06/160627_hyena_bites_boy_south_africa.shtml" platform="highweb"/></link>
Kazalika, wata jaridar kasar ta ruwaito cewa wasu gungun Zakuna sun karasa cinye sauran naman jikin mutumin.
Tuni dai 'yan sanda suka kwashe abin da ya yi saura na jikin nasa a ranar Talata da daddare.






