Ni ba ɓarauniya ba ce — Diezani

Ana zargin Diezani da tafka almundahana lokacin da take ministar man Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ana zargin Diezani da tafka almundahana lokacin da take ministar man Najeriya

Tsohuwar ministar mai ta Nigeria, Diezani Alison-Madueke ta musanta zargin da gidan Talabijin na Al jazeera ya yi mata cewa ta tafka cin hanci lokacin da take rike da mukamin.

A rahoton, Aljazeera ta yi zargin cewa Diezani Alison Madueka na da gida a Abuja da ya kai dala miliyan 18 da gwala-gwalai da darajarsu ta kai dala miliyan biyu.

Hukumar da ke Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin kasa Ta'annati, EFCC, ta kwace kadarorin tana zargin an mallake su ne da kudaden cin hanci.

Misis Alison-Madueke ta ce dama ta na da arzikinta tun kafin ta zama minista kuma za ta iya mallakar kayayyakin more rayuwa inda ta bayyana masu zarginta da cin hanci a matsayin marasa imani.

  • <link type="page"><caption> "Diezani na fama da cutar daji"</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/news/2015/10/151009_diezani_cancer_confirmed" platform="highweb"/></link>
  • <link type="page"><caption> An bada belin Diezani Alison-Madueke</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/news/2015/10/151002_diezani_madueke" platform="highweb"/></link>
  • <link type="page"><caption> Jonathan zai iya faɗa da kowa a kan Diezani — Sanusi</caption><url href="http://www.bbc.com/hausa/news/2016/05/160505_sanusi_diezani_row" platform="highweb"/></link>

Diezani ta ce "ba wannan ne karo na farko da aka yi yunkurin bata min suna a idon al'umma ba".

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, Misis Madueke ta ce rahoton wanda aka hada ba tare da wani shaida ba, an yi ne da zummar bayyana ta a matsayin mai aikata mugayen laifuka.

Ta kara da cewa "yaushe ya zamo lafi don mace mai kima irin ta wa ta mallaki gwala-gwalai".