'Yan Iran ba za su je Hajjin bana ba

Asalin hoton, Reuters
Ministan al'adun kasar Iran ya ce ba za su tura 'yan kasarsu aikin Hajji a wannan shekarar ba.
Ali Jannat ya ce ba zai yiwuwu 'yan Iran su yi aikin Hajjin ba, yana mai zargin Saudiyya da yin kafar-ungulu ga 'yan Iran da ke so su yi aikin Hajjin.
A lokacin Hajjin bara ne dai daruruwan mahajjata suka rasa rayukansu kuma akasarinsu 'yan Iran ne a turmutsitsin da aka samu wanda kasar Iran din ta dora alhakin hakan kan hukumomin Saudiya.
Ana ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen guda biyu, a yayin da kasashen ke marawa yankunan da ke yaki daban-daban baya, cikinsu har da Syria da Yemen.







