Kashi 75% na 'yan Saudiyya zasu mallaki gida

Asalin hoton, AP
Ma'aikatar samar da gidaje ta Saudiyya tace, nan da shekaru 5 kashi 75% na 'yan ƙasar zasu mallaki gida na kansu.
Wannan shiri zai samar da gidaje ga iyalai miliyan daya da rabi.
Jaridar Arab News tace yanzu za a rage tsawon lokacin samun izinin yin gini daga wata 6 zuwa wata 2.
Yanzu haka gwamnati tana gina gidaje a wurare 67 da ake son kammalawa cikin kankanin lokaci.
Jaridar ta ce, yanzu haka ana gina rukunin gidaje 66,000, kuma za a samar da gidaje 162,000.
Hukumomin na Saudiyya suna so ne su samar da gidaje ga iyalai 230,000 da kuɗin shigarsu ya gaza Riyal dubu shida kowanne wata.







