An yi jana'izar mutane 44 a Taraba

A ranar Lahadi da dare ne dai zuwa wayewar garin Litinin, maharan suka far wa kauyukan da bindigogi da kuma adduna, inda suka yi kashe-kashe da kone-kone sannan suka sulale.

Hukumomi dai na cewa sun dukufa domin bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu a aika-aikar.

Jihar ta Taraba dai ta sha fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini musamman a kananan hukumomin Wukari da Ibi, amma ba kasafai ake samun tarzoma a yankin na Gashaka ba, inmda aka yi kashe-kashen na baya-bayan nan.