Kalaman Trump na kama da na Hitler

Asalin hoton, AP
Shugaban kasar Mexico Enrique Peña Nieto shaida wa wata jaridar kasar cewa irin kalaman da Donald Trump ke yi, mai neman takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar suna kama da kalaman Adolf Hitler da Benito Mussolini.
Mr Trump dai ya yi wani furuci mai tunasarwa a kan 'yan ci-ranin da suka fito daga Mexico a yakin neman zabensa, inda ya ambaci wasu da cewa masu fyade ne, har ma ya yi alkawarin tilasta wa Mexico daukar dawainiyar gina ganuwa tsakaninta da Amurka.
Kazalika, a wata hira da wata jaridar, Shugaba Enrique Peña Nieto ya ce Mr Trump yana bata dangantakar da ke tsakanin Mexico da Amurka.







