Kun san dalilan da ke sa yawaitar mutuwar aure a Nigeria?

Wasu amare a Kano, Najeriya
Bayanan hoto, Wasu amare a Kano, Najeriya
Lokacin karatu: Minti 1

Masana da malamai sun ce talauci da rashin sanin hakkin aure da ganganci da kuma auren rashin so su ke haddasa yawan mutuwar aure a Najeriya.

Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Daurawa wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa lamarin na da matukar ban tsoro.

Ga karin bayanin da ya yi wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai:

Sai dai a cewar Sheikh Daurawa, a wasu wuraren matsalolin na raguwa saboda wayar da kan mutane da ake yi.

Ya ce yanzu fargabar ci gaba da daukar nauyin mata bayan mazajensu sun rabu da su, musamman idan matan suna da juna biyu ko 'ya'ya, tana sa wasu mazaje yin hakuri da matansu.