Lamorde ya musanta karkatar da kudade a EFCC

Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC, Ibrahim Lamorde ya musanta zargin da 'yan majalisar dattawan kasar ke yi masa na karkatar da naira tiriliyan daya.
Lamorde ya shaida wa BBC cewa zai gurfana a gaban kwamitin da majalisar ta nada domin ya gudanar da bincike a kan sa, idan an bi kaida wajen gayyatar sa.
Ya ce "Na rubutawa majalisa cewa ba zan amsa wannan gayyatar ba a yanzu, amma a nan gaba idan an bi ka'ida zan iya amsa gayyatar."
"Tun da aka kafa EFCC a shekara ta 2003, ba ta samu naira triliyan daya ba, a don haka babu gaskiya a wannan zargin," in ji shugaban EFCC.
A cewar sa, naira tiriliyan daya ba karamin kudi ba ne, don haka babu ta yadda zai sace kudi masu girman hakan.
Matakin majalisar na binciki kan Lamorde na zuwa ne 'yan makonni bayan da hukumar EFCC ta gayyaci uwargidan shugaban majalisar dattawan watau Toyin Bukola Saraki domin ta amsa tambayoyi kan zargin aikata ba daidai ba.






