Rayuwa a gidan kaso a Najeriya

Asalin hoton, AFP
" motar gidan yari ce amma sai kun bayar da kudi wai za su sayi mai...ko shekararka nawa a gidan yari idan dai suka bincika ba ka da kudi to wallahi ba za su kai ka kotu ba". In ji wani wanda ya zauna a gidan yari.
Wannan mutum wanda ya so a boye sunansa saboda yanayin tsaro ya shaida wa BBC cewa suna zama cikin matsatsi da cunkoso.
Ya ce kusan duk wanda ya zauna a irin wannan yanayi zai fuskanci cutar karzuwa sakamakon yanayin zaman.
Sai dai jami'in hulda da jama'a na hukumar gidajen yarin Najeriya, Francis Enebore, ya musanta batun karbar kudi daga firsinonin.
A baya bayan nan dai shugaban Najeriya, Muhammad Buhari ya bayar da umarnin rage cunkoso a gidajen kason kasar.






