An karrama Ado Bayero

Asalin hoton, AFP
Hukumar kula da adana kayan tarihi ta Najeriya na bikin nunin kayayyakin sarauta na marigayi Ado Bayero.
An shirya bikin ne domin karrama marigayin da kuma tunawa da irin gudunmawar da ya bayar ta hanyar bunkasa al'adun Hausawa.
Sarkin yayi fice a ado na sarauta da kuma hawan sallah na kasaita a duk shekara.
Marigayi sarkin shine mafi dadewa a gadon sarauta a tarihin Kano a yau ne ya ke cika shekara guda cif da rasuwa.







