Jirgin yaki ya kashe masu makoki 37 a Niger

Asalin hoton, AFP
Wani jirgin yaki ya kashe wasu mutane 37 da ke zaman makoki a wani kauye da ke yankin Abadam a jamhuriyar Nijar.
Mataimakin magajin garin Abadam, Ibrahim Ari wanda ya tabbatar wa da BBC aukuwar lamarin ya ce mutane fiye da 20 kuma sun jikkata a lokacin da abin ya faru a ranar Talata.
Malam Ibrahim ya kara da cewa jirgin yaki ya saki bama-bamai uku ne, daya ya fada tsakiyar masu zaman makokin, yayin da biyu kuma suka fashe a wajen gari.
Dakarun kawance da ska hada da na Najeriya da Nijar da kuma Chadi na kai farmaki kan maboyar 'yan kungiyar Boko Haram ta sama da ta kasa.
Abin da yasa wasu ke ganin jirgin mai yiwuwa jirgin ya kuskure masu zaman makokin ne da cewa 'yan Boko Haram ne.
Sai dai kakakin rundunar tsaron Najeriya, Manjo janar Chris Olukolade ya ce bashi da labarin wani jirgi na kasar ya harba bam a kan masu zaman makoki.







