Ka da Buhari ya tsaya takara a 2015 - Gumi

Asalin hoton, Getty
Wani fitaccen malamin addinnin Musulunci a Nigeria, Sheikh Ahmed Gumi ya yi kira ga tsohon shugaban Nigeria, Janar Muhammadu Buhari ka da ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekara ta 2015.
Sheikh Gumi ya bukaci Janar Buhari ya baiwa matasa dama saboda shekarunsa sun hau.
A cewarsa, 'yan siyasa na amfani da Janar Buhari ne kawai domin su cimma burinsu na siyasa saboda farin-jinin Janar din a tsakanin talakawan kasar.
Wannan shawarar na zuwa ne, mako daya bayan da Janar Muhammadu Buhari ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a karkashin tutar jam'iyyar APC mai adawa.
A shawarar da Sheikh Gumi ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kuma bukaci Shugaba Jonathan kada ya tsaya takarar a 2015 domin a samu zaman lafiya a kasar.
Kawo yanzu Janar Buhari ko magoya bayansa ba su maida martani ba game da shawarar ta Sheikh Gumi.







