Taron kasa ya ba da shawarar soke kananan hukumomi

Babban taron kasa da ake yi a Abuja a Nigeria ya ba da shawarar soke kananan hukumomi 744, a matsayin sashen gwamnati na uku na kasar.
Hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin siyasa da shugabanci da kuma tsaron kasa da aka mika ga babban zauren taron a ranar Alhamis.
Ko da ya ke taron ya kuma ba da shawarar cewa jihohi na iya kafa nasu kananan hukumomin kamar yadda suke so.
Hakan dai ya saba da kiraye-kirayen da wasu a kasar ke yi na a bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu.







