Masarautar Kano ta soke nadin Waziri

Majalisar masarautar Kano ta warware nadin da aka yi wa Sheikh Nasir Muhammad Nasir a matsayin wazirin Kano.
Babban dan majalisar sarki, Wamban Kano Alhaji Abbas Sanusi ya shaida wa manema labarai hakan a daren ranar Talata, jim kadan bayan wani taro da majalisar ta yi a fadar sarkin Kano.
Wamban Kano ya ce an dauki matakin ne saboda gwamnatin Kano ba ta goyi bayan nadin Sheikh Nasir Muhammad ba.
Gwamnatin jihar ta Kano ta yi watsi da nadin ne, saboda wani rahoto da ya muna mutane basu amince ba.







