'Yan Boko Haram sun kai hari a Kamaru

Asalin hoton, AFP
Wasu mutane da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai wa barikin jami'an tsaro na jandarma hari a birnin Kousseri na Kamaru.
Rahotannin sun ce an yi harbe-harbe da bindigogi abinda ya janyo mutuwar jami'an tsaro biyu sannan kuma 'yan kungiyar Boko Haram suka samu fidda 'ya'yansu biyu da ake tsare da su a wannan barikin.
Yankin arewacin Kamaru ya kasance inda ake tashin hankali tsakanin jami'an tsaro da 'yan Boko Haram wadanda ake zargin sun tsallaka daga Nigeria zuwa kasar ta Kamaru.
Hukumomi a Nigeria sun bukaci gwamnatin Kamaru ta basu hadin kai a kokarinsu na yaki da Boko Haram.
A cikin farko watan Afrilu aka sace wasu fadan coci a arewacin Kamaru su biyu sannan kuma a bara 'yan Boko Haram sun sace iyalan wasu Faransawa a arewacin Kamarun.






