Chibok: An kubutar da karin 'yan mata

Boko Haram Najeriya
Bayanan hoto, Boko Haram Najeriya

Sojan Najeriya sun ce sun kubutar da karin 'yan matan da aka sace a Chibok , tare da kama daya daga cikin 'yan bindigar da suka sace sun.

A cikin wata sanarwa, hedikwatar sojan ta bayyana cewar shugabar makarantar ta tabbatar da cewa, yanzu 'yan mata 8 ne suka rage a hannun 'yan bindigar, kuma suna ci gaba da kokarin gano su .

Har yanzu dai ba a san takamaimai makomar sauran 'yan mata 'yan makaranta da ake zargin kungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ba.

Sai dai wakilin BBC a Abuja ya ce, babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabbatar da wannan kuma wasu 'yan sa'oi gabanin wadannan bayanan, gwamnan jihar Borno ya fada cewar har yanzu ba a ga 'yan matan da dama ba.

A ranar Litinin ne, 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata na makarantar sakandare ta kwana da ke garin Chibok su fiye da 100.

Tun farko Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya yi tayin bada tukwicin naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada bayanai game da 'yan matan sakandare da aka sace a jihar.

A cikin hirarsa da BBC, Gwamna Shettima ya ce matakin bada tukwicin zai taimaka wajen gano inda aka kai 'yan matan da aka sace.