NEMA ta fara rabon kayan agaji a Borno

Asalin hoton, NEMA
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce ta fara raba kayan agaji ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, a wasu sassan jihar Borno.
Yankunan da aka fara rabon kayayyakin agajin sun hada da Mainok da Jakana, wadanda suka yi fama da hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa a kwanakin baya.
Al'ummomi da dama da rikicin Boko Haram din ya shafa na korafin cewa, ba sa samun wani taimakon a zo a gani, daga gwamnati ko daidaikun jama'a.
Mutane miliyan uku ne aka yi kiyasin na bukatar agajin gaggawa, akasarinsu mata da kananan yara a jihar ta Borno.






