An kai wa hukumar zabe hari a Kabul

Asalin hoton, ugc

Mayakan Taliban a Afghanistan sun kai wa hedikwatar hukumar zaben kasar hari a Kabul.

Harin ya zo ne mako guda kafin zaben shugaban kasar.

'Yan bindiga, sanye da kayan mata, sun boye bindigogi da gurnet-gurnet a cikin kayansu, su ka murkushe 'yan gadi, sa'adda su ka kai harin.

An kwashe awoyi ana ta harbe harben bindigogi da jefa bama-bamai.

Jami'an gwamnati sun ce an kashe dukkan wadanda su ka kai harin.

Tunda farko dai shugaban 'yan sanda a Kabul, Janar Mohammed Zahir, ya ce 'yan ta'adda ne su ka kai harin, kuma za a kawar dasu.

Wasu rahotanni sun ce anga wasu kayan aikin hukumar zaben sun kama da wuta.

'Yan Taliban dai sun ce sune su ka kai harin. Da man sun yi barazanar cewa za su tarwatsa zaben da za ayi a kasar ta Afghanistan.