An kashe mutane da dama a Borno da Adamawa

Asalin hoton, AFP
A Najeriya rahotanni sun ce an hallaka mutane dayawa, a wasu hare-hare biyu da ake jin masu fafutukar Musulunci sun kai a arewa maso gabashin kasar.
Mazauna wani kauyen da aka kaiwa hari a jahar Borno sun ce, akalla mutane hamsin ne aka kashe, sannan an kona gidaje masu yawa.
A hari na biyu kuma, a makwabciyar jahar Adamawa, an ce mutane fiye da ashirin ne suka hallaka, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kutsa kai a cikin wata coci:
A jihar Adamawa ta Najeriya wasu 'yan bindigar sun kashe mutane ashirin da shida a garin Cakawa da ke Karamar Hukumar Madagali.
Wannan hari na jihar Adamawan an kai shi ne a jiya.







