Za a daina amfani da kudi na 'leda' a Nigeria

Za a koma amfani da kudin takarda a Nigeria, don kawo karshen amfani da wasu kudi na leda.
A shekara ta 2007 ne aka mayar da naira 5 da 10 da 20 da 50 suka zama na leda.
Amma a yanzu bayan shekaru shida, za a mayar da kudin su kara komawa na takarda.
Babban bankin Nigeria- CBN wanda ya bada sanarwar, ya ce sun gano cewar yanayi na zafi a Nigeria na saurin lalata takardun kudin na leda.
A halin yanzu dai kudaden da suke na takarda a Nigeria sune; 100, N200, N500 da kuma N1,000.
Kakakin CBN Ugochukwu Okoroafor, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar "kudi na leda na saurin kodewa".







