Matsalar yawan fyade a Najeriya

A Najeriya mata a jahar Kaduna sun tashi tsaye wajen yakar masu yi masu fyade.
Lamarin fyade matsala ce da ake kara fuskanta a Najeriyar.
Wata kungiya mai suna Peace and Revival Foundation ta gudanar da taro a Kaduna, inda ta yi kira ga shugabannin addinin Krista da Musulmi da su ware wasu lokuta don yin wa'azi a kan illolin fyade.
Matan sun kuma bukaci gwamnati da ta bullo da tsauraran dokoki domin hukunta masu yin fyaden.
Suka ce, masu yin fyaden na lalata rayuwar mata saboda ba a bari a kwashe daidai.







