PDP za ta yi taron dinke baraka

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan zai gana da gwamnonin jam'iyyar PDP, domin nemo bakin zaren warware barakar jam'iyyar.
Za a yi ganawar ce a fadar shugaban kasar dake Abuja a ranar Talata.
Yunkurin sasantawa da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya kira a makon jiya, bai yi nasara ba.
Masu sharhi dai na ganin, idan ba a hanzarta magance rikincin da jam'iyyar ta tsinci kanta a ciki ba, to zai iya jefa kasar cikin rudani.
Yanzu haka dai, wasu 'yan majalisar dittajai da kuma na wakilai sun riga sun yi mubaya'a ga bangaren shugabancin daya balle na PDP.
Alhaji Bamanga Tukur ne shugaban PDP dake samun goyon bayan fadar shugaban kasa, a yayinda Alhaji Abubakar Kawu Baraje ke jagorantar bangaren gwamnoni bakwai da suka balle.







