APC ta dade tana hasashen baraka a PDP

Wasu jagororin babbar Jam'iyar adawa ta APC a Najeriya, sun fara tofa albarkacin bakinsu game da rikicin jam'iyya mai mulki ta PDP.
Sanata Lawal Shu'aibu, jigo ne a Jam'iyar adawa ta APC ya ce dama sun dade suna hasashen hakan zai faru ga jam'iyyar mai mulki.
Sanata Lawal ya kuma ce APC na maraba da bangaren jam'iyyar PDP da ta balle.
Sai dai sabon mataimakin PDP, Barrister Ibrahim Abdullahi Jalo, ya musanta cewa akwai baraka a PDP.







