An kashe 'yan sanda biyu a Kajuru

'Yan sanda Najeriya
Bayanan hoto, 'Yan sanda Najeriya

Rundunar 'yan sanda jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar jami'anta biyu yayinda wasu suka samu raunuka, a wani hari da 'yan bidiga suka kaddamar a kan wani caji ofis a karamar hukumar Kajuru.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Olufemi Adenike wanda ya tabbatarwa da wakilinmu Nurah Muhammed Ringim, ya ce kawo yanzu ba a gano wadanda suka kai harin ba.

Rahotanni dai na cewa, an shafe sao'i da dama ana yin musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindigar da suka afkuwa ofishin 'yan sanda na garin Kajurun.

Jihar Kaduna dai ta sha fama da kalubalen tsaro dake haddasa hasarar rayuka.