Boko Haram ta fitar da wani sabon sakon bideo

Imam Abubakar Shekau
Bayanan hoto, Imam Abubakar Shekau

Wani sabon faifan video da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya sami kwafi ya nuno shugaban kungiyar Jamaa'tu Ahli Sunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, Imam Abubakar Shekau, yana ikirarin cewa dakarunsu sun fatattaki sojojin gwamnatin Najeriya a wurare da dama.

Hakazalika, Imam Shekau ya yi kira ga masu jihadi a kasashen Afghanistan da Pakistan da kuma Iraqi da su je Najeriya domin taimaka masu a gwagwarmayar da suke ta kafa wata daular musulunci a kasar.

Makonni biyu kenan da gwamnatin Najeriya ta kafa dokar ta baci a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, sakamakon kashe kashen da ke faruwa a can.

Gwamnatin ta tura dubban sojoji zuwa yankunan domin murkushe masu tada kayar bayan.

Wannan furuci na Imam Shekau dai ya ci karo da ikirarin da hukumomin tsaro a Najeriyar suke yi, cewa suna samun nasara sosai wajen yaki da mayakan na Boko Haram, wadanda suke zargi da haddasa fitina a kasar.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin da duka bangarorin biyu suka yi.