Kwamandan Sojin Syria ya sauya sheka

Rahotanni daga Syria sun ce kwamandan sojojin Syria ya sauya sheka daga bangaren gwamnati zuwa na 'yan tawaye.
Tashar talabijin ta Al Arabiya ta watsa wata murya da ta ce sanarwa ce daga Manjo Janar Abdulaziz al-Shalal inda a ciki ya ce rundunar sojojin Syria ta kauce daga jigon aikinta na kare kasar, ta koma rundunar gungun masu kisa.
Da ma dai wadansu kafofin 'yan adawa sun sanar cewa kwamandan ya koma bangaren 'yan tawaye.
Janar Shalal shi ne jami'in soji mafi girma da ya sauya sheka tun lokacin da aka fara rikicin na Syria shekaru biyu da suka gabata.







