China ta bude layin dogo mafi tsayi a duniya

China ta bude wani layin dogo mafi tsayi a duniya kuma mai gudun gaske daya tashi daga babban birnin Beijing zuwa birnin Guangzhou dake kudancin Kasar
Jirgin Pasinja na farko ya bar Beijing a ranar laraba da safe, a wata tafiya ta kusan kilomita 2,300
Tsawon lokacin da ake dauka wajen tafiyar zai ragu daga fiye da sa'oi ashirin zuwa sa'oi takwas
Shekaru biyar da suka gabata ne dai Chinan ta soma amfani da irin wadannan jiragen Kasa masu gudun gaske
Amma aikin ya gamu da cikas na zarge zargen cin hanci da kuma rikicin da akai ta samu kan tsaron lafiyar tafiya a jiragen







