Sabbin matakan yaki da cin hanci a China

Gwamnatin kasar China ta bayyana wasu sabbin matakan da zata dauka domin shawo kan almubazzaranci da manyan sojoji ke yi a matsayin wani bangare na matakan da sabuwar gwamnatin ta dauka na yaki da cin hanci.
Sabbin matakan sun hada da rage yadda ake almubazzaranci da kudi a wajan tarukan janar janar da sauran manyan sojoji.
Wakilin BBC ya ce daga yanzu ba batun shinfida jajayen dardumai da yin wasu wasanni ko faretin girmamawa a wajan tarukan manyan sojoji.
Hakanan kuma za'a rage barasar da ake samarwa a lokacin.
Har ila yau za'a takaita amfani da jiniya a motocin sojoji kuma an baiwa manyan jami'ai umarnin hana 'yan uwansu karbar cin hanci.







