
Patience Jonathan
A Najeriya, gidan talbijin na kasar ya nuna uwar gidan shugaban kasar, Mrs Patience Jonathan inda ta tabbatarwa da 'yan kasar cewa ba ta fama da matsananciyar rashin lafiyar da har wasu zasu iya cewa tana kwance rai kwakwai mutu kwakwai.
Mrs Jonathan na magane ne jim kadan bayan da ta dawo daga kasar Jamus inda ta je yin jinya.
Tun a watan da ya gabata ne dai aka daina ganinta a bainar jama'a, lamarin da ya haifar da jita-jita a tsakanin 'yan kasar da wasu kafafen yada labarai.
Mrs Jonathan ta yi godiya ga Allah kasancewar ya sa ta dawo gida, sai dai ba ta yi karin bayani ba akan koshin lafiyarta.
















