Najeriya ta cika shekaru 52 da 'yancin kai

An sabunta: 1 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:49 GMT

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan


A yayinda Najeriya ke bikin cika shekaru hamsin da biyu da samun 'yan cin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya; shugaban kasar Goodluck Jonathan ya yi jawabi ga alummar kasar.

Jawabin da ya yi a kafar yada labarai na gwamnatin kasar ya yi bayanin kokarin da gwamnatin ta yi kan inganta samar da wutar lantarki, da fannin lafiya da ma tsaro.

Shugaban ya ce bayan taaziya da yake yi ga wadanda suka rasa rayukansu a rikicin hare-hare na bama-bamai da na bindigogi shugaban ya ci layar kare rayukan jamaa da dukiyoyinsu.

Ya kuma ce gwamnatinsa na saka kaimi wajan hana yawaitar makamai a hannun farar hula da kuma shigo da su.

A cewar Shugaba Goodluck Jonathan kasar ta yi rawar gani a fannin lafiya abinda ya sa ta rage yawan mata masu mutuwa yayin da suka zo haihuwa da kuma kananan yara masu mutuwa 'yan kasa da shekaru biyar.

Sai dai yayin da shugaban ke wadannan kalamai wasu kungiyoyin dake fafutikar yaki da talauci a kasar sun bayyana damuwarsu game da irin halin rayuwar da talakawan kasar ke ciki.

A wata sanarwa da kungiyar agaji ta Action Aid ta bayar, kungiyar ta ce har yanzu 'yan kasar na ci gaba da rayuwa cikin matsanancin talauci duk kuwa da irin albarkar da Allah ya yiwa kasar ta fannin noma da man fetur.

Ita ma kungiyar dake fafutikar kare hakkin bil'adama ta SERAP a wata sanarwar da ta fitar don bikin cikar Najeriya shekaru hamsin da biyu da samun 'yancin kai, ta yi kira ga mahunkuntan kasar da su zage dantse don ganin sun inganta rayuwar jama'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.

]]>