
Farfesa Barth Nnaji
Ministan ma'aikatar samar da hasken wutar lantarkin Najeriya, Farfesa Barth Nnaji, ya yi murabus.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin yada labarai, Reuben Abati, ya fitar ya ce shugaban kasar Goodluck Jonathan ya amince da murabus din ministan nan take.
A cewar sanarwar, shugaban ya yaba wa ministan bisa bautawa kasar a karkashin mulkinsa, kuma ya yi masa fatan alheri.
Babu dai cikakken bayani a kan dalilan murabus din na Farfesa Nnaji.
'Yan Najeriya sun kwashe shekaru da dama suna fama da karancin wutar lantarki.
Gwamnatoci da dama sun sha alwashin kawo sauyi a fannin samar da wutar lantarki amma har yanzu hakar su ba ta cimma ruwa ba.
















