
Shugaba Goodluck Jonatthan
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2013 na sama da naira trillion hudu a gaban zauren Majalisar Dokokin kasar a Abuja.
Kasafin kudin na badi ya zarta kasafin kudin bana da kimanin kashi biyar cikin
dari.
Shugaba Jonathan ya ce an tsara kasafin kudin badin ne akan dala sabain da biyar akan kowace gangar mai, kuma kudaden shigar kasar gabaki daya zai karu da kashi shida da digo shida.
Sai dai kakakin Majalisar wakilai ta Najeriya Aminu Waziri tambuwal, ya ce sun kara kudin gangar man zuwa dala tamanin domin amfani da rarar kudin da za a samu wajen rage basussukan cikin gida da ake bin kasar.
Kasafin kudin badin na nuni da cewa kudaden shigar kasar zai cigaba da habaka daga bangaren da ba na man fetur ba.
Haka kuma shugaba Jonathan ya ce za'a kara wa bangaren manyan ayyuka kaso daga kasafin kudin fiye da abin da aka ware masa a kasafin kudin bana.
















