
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya ya yi jawabi ga 'yan kasar kai tsaye a safiyar yau Talata, inda yayi alkawarin bawa Jihohin da ambaliyar ruwa ya shafa naira biliyan goma sha bakwai da miliyan dari shida.
Shugaban Goodluck Jonathan ya yiwa 'yan kasar jawabi kan ambaliyar ruwan da ya shafi wasu Jihohi a kasar da kuma hobbasar da gwamnatin ke yi na rage radadin ambaliyar ga wadanda alamarin ya shafa.
Ambaliyar ruwan dai ta hallaka mutane da dama ta kuma lalata dukiyoyin jama'a gami da tafiya da gonaki da dabbobi.
Sai dai dama Hukumar dake kula da hasashen yanayi a kasar tayi hasashen cewa za'a sami ruwa mai yawan gaske da kuma yiwuwar samun ambaliyar ruwa.
Gwamnatin kasar ta ce ta kasa Jihohin ne da ambaliyar ruwan ya shafa rukuni-rukuni don raba musu kudaden da zai rage radadin ambaliyar.
















