
Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sauya shugabannin rundunonin sojan ƙasar na sama, da ruwa da kuma na ƙasa.
Yanzu dai Vice Admiral, O.S. Ibrahim shi ne babban hafsan hafsoshin rundononin tsaron ƙasar, kuma ɗan jihar Kwara ne da a da yake riƙe da shugancin rundunar sojan ruwa.
Kuma an naɗa Rear Admiral, D.J. Ezeoba, wanda ya fito daga jihar Delta a matsayin sabon babban hafsan sojan ruwan Najeriya.
An kuma naɗa Air Vice Marshall, Alex Badeh, wanda ya fito daga jihar Adamawa a matsayin sabon babban hafsan sojan sama na Najeriya.
Shi kuma Laftanar janar, O.A. Ihejirika, dan jihar Abia, zai cigaba da kasancewa a matsayinsa na babban hafsan sojan ƙasa.
A wata sanarwa da ya sanyawa hannu, kakakin shugaban Najeriyar, Reuben Abati yace, shugaba Jonathan ya godewa waɗanda aka sauƙe daga kan muƙamansu.
















