
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar cewa, za su hada karfi da takwarorinsu na Tarayyar Nijeriya, su karfafa matakan tsaro don yaki da kungiyoyi irin su Alqa'ida da Jama'atu Ahlis Sunna lid Da'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram.
Matakan dai sun hada da sintirin jami'an tsaro a kan iyakokin kasashen biyu.
Ministan shari'a, kuma Kakakin gwamnatin Nijar, Malam Marou Amadou, shi ne ya tabbatar da haka a birnin Yamai, a lokacin da hukumar karfafa hulda tsakanin Nijar da Najeriya ta yi taronta Yamai a karshen makon jiya.
















