
Issoufou Mahamadou, shugaban Niger
Hukumomi a jamhuriyar Niger sun girke dakarun tsaro a majami'u dake birnin Yamai, domin kaucewa tashin hankali dangane da fim din nan na batanci ga musulunci da ya haddasa tarzoma a kasashe da dama.
Ko a daren jiya ma dai jami'an taso sun tarwatsa wasu malaman addinin musulunci da suka so yin wa'azi a Yamai domin kalubalantar fim din.
A karshen mako ma dai wasu masu zanga-zanga dangane da batun fim din na batanci sun kona wasu majami'u a birnin Damagaram.
Wannan batu dai na cigaba inda Amurka aka ce, jami'an tsaro sun yi tambayoyi ga mutumin da ake zargin shi ya shirya fim din.
















