
Wasu jami'an tsaron Nijeriya
Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a Jihar Yobe dake Arewacin Najeriya, wato JTF, ta ce ta harbe wasu 'yan bindiga kimanin 36 a wata arangama da suka yi daga jiya lahadi zuwa safiyar yau Litinin.
Hakazalika, rundinar ta ce ta kama wasu karin 'yan bindigar fiye da dari da hamsin a wasu jerin farmaki da ta kai a jihohin Adamawa da Yoben.
Kakakin rundunar ta JTF a jihar Laftanar Eli Lazarous ne ya tabbatar da haka a wata hira da manema labarai yau a birnin Damaturu.
Hakan dai ya faru ne duk da cewa dokar takaita zirga-zirga ta ba dare-ba-rana na aiki a jihar ta Yoben, tun a ranar Juma'ar da ta gabata.
Jihar ta Yobe dai na daga cikin johohin Arewacijn Nijeriya da aka sha kai hare-hare, wadanda ake dangantawa da kungiyar nan ta Jama'atu Ahli Sunna Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram.
















