
Shugaban kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna Lil da'awati wal jihad, wacce ake kira Boko Haram, Imam Abubakar Shekau
Rahotanni daga Kano a arewacin Nigeria sun ce rundunar hadin gwiwa ta JTF ta kaddamar da wani hari a yau, a kan wasu manyan shugabannin kungiyar Jama'atu Ahlus Sunna Lidda'awati wal Jihad wacce ake kira Boko Haram.
Rahotannin sun ce an hallaka daya daga cikin yan kungiyar a farmakin da rundunar ta JTF ta kai.
Rundunar tsaro ta JTF a Kano ta tabbatar da cewar ta kai wannan farmaki, inda ta kama mutane biyu.
Kakakin rundunar ta JTF a Kano ya ce daya daga cikin mutanen da aka kama ya mutu a asibiti.
Rundunar ta ce ta na gudanar da bincike domin tantance ko wanene mutumin da ya mutu.
Wata majiya ta ce mutumin da ya rasu shine mai magana da yawun kungiyar ta Boko Haram, wato Abu Qaqa.
Sai dai har zuwa wannan lokacin kungiyar ta Jama'atu Ahlus Sunna Lid da'awati wal Jihad ba ta ce komai ba dangane da wannan lamari.
A can baya, hukumomin Nigeria sun taba bayyana cewar sun kama Abu Qaqa, amma daga bisani kungiyar Boko Haram ta ce Abu Darda ne aka kama ba Abu Qaqa ba.
















