
Shugaban kasar Sudan Al Bashir
Sojojin gwamnatin Sudan sun gwabza fada da 'yan tawaye a yammacin yankin Darfur.
Sojojin sun ce sun kashe 'yan tawayen talatin da biyu lokacin da masu tayar da kayar-bayan suka kai hari a wani Kauye dake kan dutse.
Amma kungiyar 'yan tawayen Justice and Equality Movement ta ce ta kashe sojojin masu dimbin yawa wadanda suka kai hari a kan Kauyen bayan mayakan sama na kasar ta Sudan sun yi wa yankin ruwan bama-bamai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rashin jituwa kan tsaga iyakoki tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu ke neman sake jefa su cikin yaki.
















