
Ministan harkokin addini na Sudan, Ghazi Al-Sadiq
A Sudan wani jirgin sama mai dauke da mutane talatin da daya wadanda suka hada da shugabannin soji da na siyasa ya yi hadari.
Ministan harkokin addini na kasar, Ghazi Al-Sadiq yana cikin wadanda hadarin ya rutsa da su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa bukukuwan sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.
Jirgin dai ya yi karo ne da wani tsauni da ke kusa da Talodi a kudancin Kordofan.
Rashin kyawun yanayi ne dai ya hana jirgin sauka a karo na farko da ya yi kokarin yin hakan, amma sai ya yi hadari yayin da ya yi yunkurin sauka a karo na biyu.
















