An hallaka sojojin Sudan ta Kudu ashirin da hudu

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:33 GMT
Sojojin Sudan ta Kudu

Sojojin Sudan ta Kudu na kan hanyar tafiya gudanar da aiki

Wani babban jami'in gwamnatin Sudan ta Kudu ya ce 'yan tawaye sun hallaka akalla sojojin gwamnati ashirin da hudu, tare da jikkata goma sha biyu a jihar Jonglei.

Gwamnan jihar, Kuol Manyang ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran kasar Faransa cewa harin ya faru ne ranar Alhamis, amma wadanda suka tsira da ransu ne suka bayar da rahoton abin da ya faru.

Rashin tsaro na daya daga cikin manyan matsalolin Sudan da Kudu, kuma jihar Jonglei nan ne lamarin ya fi kamari.

Sojojin Sudan ta Kudun na cikin dakarun da aka girke a wasu kauyuka domin gano madugun 'yan tawaye David Yau Yau wanda ya sauya sheka daga dakarun Sudan ta Kudun a cikin watan Aprilu.

Mista Mayang ya ce akwai karin wasu sojojin 17 da suka bace, yayin da 12 suka jikkata, kana wasu fararen hula dake yankin sun shiga cikin kai harin.

Kodayake lamarin ya faru ranar Alhamis, amma an dauki tsawon lokaci kafin a samu labarin, saboda wadanda suka tsira da rayukansu sun tako da kafa ne daga yanki.

Mista Yau Yau dai ya fito ne daga kabilar Murle, kabilar da matasanta suka sha nana cewa gwamnati ta maida su saniyar ware.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi dakarun gwamnatin da aikata cin zarafin bil adama yayin gudanar da aikinsu a jihar Jonglei, sai dai gwamnan jihar Mista Manyang ya musanta zargin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.

]]>