
Susan Rice
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice ta ce, duk wata rashin jituwa da aka samu a kan batun tsaga kan iyaka, za ta iya mayar da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu fagen yaki.
Mrs Rice ta ce gwamnatin Sudan har yanzu ta ki yarda da layin kan iyaka da aka shata a shirin zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afrika.
Sojojin Sudan din da na Sudan ta Kudu sun sha gwabza fada tun lokacin da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kanta a bara.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai iya barazanar garkamawa kasashen biyu takunkumi idan suka kasa amincewa da fitar da wani yanki da aka haramta harkokin soji a kan iyakokin su.
















