Shugaban kasar Mali yayi garan bawul

Shugaban kasar Mali, Traore

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaban kasar Mali, Traore

Shugaban kasa na wucin gadi a kasar Mali Diocounda Traore ya ba da sanarwar sauye-sauye da dama a gwamnatin sa wadanda suka mayar da Prime Minista Cheikh Modibo Diarra saniyar-ware.

Lokacin da yake magana a gidan talabijin na kasar Mr Traore ya ce shi da kan sa zai jagoranci shawarwari da nufin kafa gwamnatin hadin kan kasa watanni hudu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya raba kasar gida biyu.

Shugaban kasar ya yi kira ga 'yan kasar su goyi bayan duk wani kokarin da za a yi na kawo karshen rikicin siyasar da aka shiga.

Yace, "ganin sarkakkiyar wannan rikici da wahalhalun da mutane suka shiga musamman a arewaci da kuma sauran sassan kasa, a matsayin ku na masu kishin kasa ku zo mu hadu mu ceci kasar mu.