Rufewa
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na musamman kuma kai-tsaye daga Najeriya da sauran sassan duniya na 10/06/25
Haruna Kakangi, Ahmad Bawage, Aisha Babangida da Aisha Aliyu Jaafar
Mun zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

An yanke wa wata mata ƴar Birtaniya hukuncin ɗauri na shekara biyu da watanni uku a gidan yari saboda rawar da ta taka a cikin wata ƙungiya ta masu azabtar da birrai ta duniya.
An gano cewa matar mai suna Natalie Herro da ke Airdirie a kusa da yankin Glasgow ta taimaka wajen jagorantar wata ƙungiya da ke Amurka wadda ke biyan mutane a Indonesia su azabtar da birrai.
Ta wallafa ɗaruruwan hotuna da bidiyo a kan intanet na yadda suke azabtar da birran.
Ƴan sanda sun ce wannan na daga ciki manyan abubuwan da suka gani da ya tayar musu da hankali.
Wannan hukunci da kuma bincike na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da irin wannan laifin.

Asalin hoton, MINISTRY OF HEALTH
Gwamnatin Najeriya ta ce akwai yiwuwar za a samu raguwar mace-macen mata masu juna biyu a yayin haihuwa da kashi 20 cikin ɗari kafin nan da shekarar 2027.
Ƙaramin minstan Lafiyar Najeriya Iziaq Salako ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnatin ƙasar na kuma ƙokarin cimma muradin ganin an samu raguwar mutuwar jarirai da yara ƴan ƙasa da shekaru biyar da kimanin kashi 15 cikin ɗari.
Gwamnatin ta bayyana matakai daban daban da za su taimaka wajen cimma hakan kamar samar da kayan aiki, da horo ga Jam'ian lafiya.
Wata ƙwararriya a fannin kula da lafiyar mata ta ce hakan abu ne mai yiwuwa ganin irin matakan da gwamnati ta ɗauka a baya bayannan kamar kula da lafiya kyauta, da samar da motocin ɗaukar marasa lafiya cikin gaggawa, da kuma gano yankunan da ke da yawan mace-macen mata domin lalubo musabbabin hakan don magance shi.
Rahotanni na bayyana cewa gwamnatin Najeriya dai na ware kashi 5 cikin 100 ne kawai a fannin lafiya wanda bai kai kashi 15 da aka nemi kowacce ƙasa a Afirka ta ware ba.
Najeriya dai ƙasa ce da aka fi samun mace-macen mata masu juna biyu a duniya, kamar yadda wani bincike da BBC ta gudanar ya tabbatar.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban gwamnatin Austria, Christian Stocker ya bayyana harbi a makarantar sakandire a Graz a matsayin mummunar rana a tarihin ƙasar sa.
Wani ɗan bindiga ya harbe mutane 9, da dama daga ciki ɗalibai a makarantar.
Mace ta 10, ta mutu a asibiti sakamakon raunuka, ya yinda wasu 11 kuma suka jikkata.
Wanda ake zargi da harbin ɗan Australiya ne mai shekaru 21, kuma ya kashe kansa.
Mahukunta sun yi imanin shi kaɗai ya aikata ta'asar.
Sun ce tsohon ɗalibi ne a makarantar amma bai kammala karatu ba, sun kuma ƙara da cewar ya yi amfani da bindigar da aka amince a iya mallakarta.
An keɓe kwanaki 3 don alhini.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce jami'an tsaron tarayya zasu ci gaba da zama a Los Angeles har sai an tabbatar babu sauran hatsari.
Ɗaruruwan sojojin ruwan Amurka sun isa Los Angeles bisa umarnin Mista Trump, wanda ke ƙoƙarin kwantar da tarzoma a birnin sakamakon kamar baƙin haure.
Ya yinda ta ke amsa tambayoyin ƴan jarida, magajin garin Los Angeles Karen Bass ta ce ana tarzoma ne a rukunin wasu gidaje a gefen gari.
Bass ta yi kira ga gwamnatin Trump da ta dakatar da kamen baƙin haure.
Magajin Garin Los Angeles Karen Bass ta ce iyalai a fadin gari sun firgita, ta kuma ce suna da mutanen da aka tsare, da kuma mutanen da ba su tuntubi lauyoyinsu ba, don haka a cewar ta akwai damuwa sosai.
Mista Trump ya kare kansa da cewar sama da ƙasa za ta haɗe inda bai aika da dakaru ba.
Wani jirgi maras matuƙi na Isra'ila ya kashe mutum guda tare da ɗansa, ya kuma jikkata wani ɗan nasa a Kudancin Lebanon, a hare-haren baya bayan nan duk da tsagaita wutar da aka cimma a watan Nuwamba.
Sojojin Isra'ila sun ce mutumin da aka kashe ma'aikacin Hezbollah ne kuma mamba a wani kamfanin ƴan tawaye a Lebanon.
Dakarun Isra'ila sun yi iƙirarin mutanen biyu na da hannu wajen bai wa Hezbollah makamai da sanyawa dakarun Isra'il da ke yankin ido.

Asalin hoton, Getty Images
Mai shekaru 15 da ake zargi da yunƙurin kashe ɗan takarar shugabancin ƙasar Colombia Miguel Uribe ya ƙaryata zargin da ake masa.
Matashin ya bayyana a Kotu inda aka tuhume shi da yunƙurin kashe Mista Uribe wanda aka harba sau biyu a ka ya yin yakin neman zaɓe a ƙarshen mako.
Likitoci sun ce ɗan takarar na cikin yanayi mai wahala.

Asalin hoton, KwaZulu-Natal government
Ambaliya a Afirka ta Kudu ta tafi da wata ƙaramar motar safa ɗauke da yara ƴan makaranta, a cewar mai magana da yawun gwamnatin lardin gabashin Cape a hirarta da BBC.
Khuselwa Rantjie ta ce zuwa yanzu ba a tabbatar da yara nawa ne ke cikin motar ba, sai dai zuwa yanzu an gano yara uku da ran su.
A cewar ta a yanzu an dakatar da aikin ceto saboda dare ya yi kuma za a cigaba a gobe Laraba.
A wani labarin na daban, an gano gawarwakin mutane bakwai da ruwa ya tafi da su a yankin OR Tambo da ke lardin.
Afirka ta Kudu dai na fama da yanayi na dusar ƙanƙara, da mamakon ruwan sama da kuma iska mai ƙarfi wanda ya kai ga rasa rayuka da kuma katse lantarkin gidaje aƙalla 500,000.
Ministan al'adu na Ukraine ya ce majami'ar St Sophia ɗaya daga cikin gine-gine masu muhimmanci a tsakiyar Kyiv ta lalace, sakamakon luguden wutar Rasha a baya-bayan nan.
Mykola Tochytsky ya ce an kai wa hasumiyar majami'ar hari, inda hotunan bidiyo suka nuna kayan ado a ƙasa.
Ukraine ta bayyana yadda aka kai mata hari da jirage marasa matuka da makamai masu linzami fiye da 300.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya buƙaci Amurka da ƙasashen Turai su ɗauki tsattsauran mataki kan yawaitar hare-haren da Rasha ta ke kai wa.
An samu rahoton mutuwar mutum biyu, inda Moscow ta ce ta kai wa sansanin sojoji hare-hare.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Birtaniya ta sanya takunkumai kan ministocin Isra'ila biyu masu tsattsaurar ra'ayi saboda ''kitsa tayar da rikici kan Falasɗinawa a lokuta da dama'' waɗanda ke gaɓar yamma da aka mamaye.
An haramtawa Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich shiga Birtaniya, kuma za a kwace duk wasu kadarorin su da ke Birtaniya a matsayin wani ɓangare na takunkuman da sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya sanar.
Lammy ya ce ministan harkokin kuɗi na Isra'ila Bezalel Smotrich da ministan tsaron cikin gida Itamar Ben-Gvir sun tunzura tayar da rikici mai muni da kuma cin zarafin falasɗinawa.
Takunkuman mataki ne na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Birtaniya da Norway da Canada da New Zealand.
Tun a baya an sha sukan Smotrich da Ben-Gvir saboda matsayarsu kan yaƙin da ake yi a Gaza.
Ministocin biyu sun hana shigar da agaji cikin Gaza kuma sun yi ta kiran a sake tsugunar da Falasɗinawa.

Asalin hoton, Others
Shugaban gwamnatin milkin sojan ƙasar Burkina Faso , Kyaftin Ibrahim Traore wanda yayi zargin cewa , manyan ƙasashen duniya na neman ingiza ɗaya daga cikin ƙasashe uku mambobin ƙungiyar AES ya ci amanar sauran.
Shugaban dai bai fito fili ya zargi wata ƙasa ba sai dai ya ce gargaɗi ne bayyananne game da ƙoƙarin kutsawa da ƙasashen ke yi tsakaninsu.
Kyaftin Ibrahim Traoré, ya bayyana zargin ne yayin bikin rera taken ƙungiyar AES a karon farko a fadarsa da ke Ouagadougou, inda ya yi tir da abin da ya ce yunƙurin tilasta wa ɗaya daga cikinsu wajen yaudara da cin amanar sauran.
Matashin shugaban ya gargaɗi sauran mambobin ƙungiyar da su shiga taitayinsu cewa ka da wanda ya bari bango ya tsage da zai bayar da ƙofar wargaza ƙungiyar.

Asalin hoton, X
A yau ake sa ran gudanar da binciken sanadin mutuwa kan gawar wani malami kuma wani mai yaɗa labarai a shafukan intanet , Albert Ojwang, wanda ya mutu yana tsare a hannun ‘yansanda – lamarin da ya janyo zanga-zanga da kuma sake haifar da ce-ce-ku-ce kan cin zarafin ‘yansanda a ƙasar.
Ojwang ya rasu a ƙarshen mako ne kuma rahotanni na nuna cewa ya samu rauni a kansa yayin da yake cikin caji ofis na ƴansanda.
Mutuwarsa ta haifar da fushi da damuwa daga jama’a, inda da dama ke zargin an lakaɗa masa shegen duka.
An kama Ojwang ne bayan da ya wallafa wasu saƙonni a dandalin sada zumunta na X da ke sukar wani jami’in ƴansanda.
Wannan mataki ya haifar da ce-ce-ku-ce da kuma wasu zanga-zanga, duk da cewa ba su da yawa, a gaban ɗakin ajiyar gawa da ke Nairobi a ranar Litinin.
Hukumomi sun ce za su fitar da cikakken bayani kan musabbabin mutuwar Ojwang bayan kammala binciken da likitoci za su gudanar a yau.
Ana sa ran wannan rahoto zai fito da ƙarin haske kan mutuwar malamin.

Asalin hoton, AFP
Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ta sake yin gargaɗi game da shiga matsalar yunwa a Sudan, musamman ma yankuna a kudancin Khartoum, babban birnin ƙasar.
Shugaban hukumar, Laurent Bukera ne ya bayyana haka, inda ya ƙara nuna damuwa kan halin d amutane ke ciki.
Yaƙin basasa tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF - ya tilastawa miliyoyin mutane tserewa daga muhallansu.
Har yanzu dai ana ci gaba da gwabza yaƙi.
A watan da ya gabata, hukumar agajin gaggawa ta duniya ta yi gargaɗin cewa amai da gugawa na dab da ɓarkewa a ƙasar.

Matar tsohon shugaban Najeriya, Maryam Sani Abacha ta musanta zarge-zargen da ake yi na cewa mijinta Janara Sani Abacha ya kwashe tare da jibge dukiyar ƙasar a ƙasashen ƙetare ta hanyar rashawa.
Maryam Abacha ta ɗauki wannan matakin ne a tattaunawar da ta yi da kafar talabijin ta TVC a ranar Litinin, shekara 27 bayan rasuwar mijin nata.
Abacha ya mulki Najeriya ne daga shekarar 1993 zuwa 1998, sai dai duk da cewa gwamnatoci sun sha bayyana cewa an dawo da wasu kuɗin da ake zargin ya ajiye a ƙasar waje, ba a taɓa tuhumar sa da rashawa ba a kotu.
Sai dai gwamnatoci da dama sun sha yin iƙirarin karɓar kuɗaɗen da ake alaƙantawa da Abacha daga ƙasashe daban-daban na duniya.
A tattaunawar, Maryam ta ce "Akwai wanda ke da shaida ko ya sa hannun cewa (Abacha) ya kwashe kuɗin Najeriya ya jibge a ƙasar waje? Ya kamata mu daina ɗora wa mutane laifi (Babu hujja).
Hajiya Maryam ta ce yawancin kuɗaden da ake cewa an mayar wa Najeriya, kuma ake alƙantawa da Abacha, ana yi ne da gangan, amma "kuɗaɗe ne da ya fitar domin ci gaban Najeriya".

Asalin hoton, STATE HOUSE NG
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa Abuja, babban birnin ƙasar bayan kwashe sama da mako biyu a Legas, domin bikin babbar Sallah.
Mai magana da shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na X cewa Tinubun yanzu haka na kan hanyar komawa Abuja.
Bayan hutun sallah, Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyuka a lokacin da yake Legas, ciki har da na katafaren aikin gina titin gaɓar teku mai tsawon kilomita 700 wanda ya tashi daga Legas zuwa Calabar.
Haka nan ya halarci bikin cikar ƙungiyar haɓɓaka tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (Ecowas) shekara 50 da kafuwa.

Rundunar sojin sama ta Najeriya karkashin Operation Haɗin-Kai, ta ce ta hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da lalata muhimman kayakinsu a yankin Tafkin Chadi.
Hakan na zuwa ne a ci gaba da yaki da ƴan ta'adda a yankin, inda sojojin suka ƙaddamar da farmakin sama a Bukar Meram, wani sansanin horo da ƴan ta'addan ke mafaka a ciki a jihar Borno.
A cewar sanarwar da Ehimen Ejodame, daraktan hulɗa da jama’a na sojojin saman ya fitar, ta ce an kai harin ranar 9 ga Yunin 2025, bayan samun bayanan sirri da suka tabbatar da ayyukan ta’adda a wajen.
Kayan da suka lalata sun haɗa da wuraren ajiye makamai da kuma sansanoni da suka kafa.
Rahoton Battle Damage Assessment (BDA) ya tabbatar da cewa farmakin ya daƙile wata barazana mai tsanani da ‘yan ta’addan ke shirin kai wa garuruwan Marte da Monguno.
Rundunar ta NAF ta ce wannan hari wani ɓangare ne na matakan riga-kafin da take ɗauka don hana ‘yan ta’adda damar sake kafa sansanoni ko kai hari a yankunan da aka ƙwato.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Dr. Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa ƙaruwar cutar ƙyandar biri wato Mpox har yanzu na cika sharuddan kasancewa cuta mai matuƙar haɗari a faɗin duniya kamar yadda kwamitin kiyaye dokokin harkar lafiya na duniya (IHR) suka tanada.
Wannan sanarwa ta biyo bayan taro na hudu da kwamitin gaggawa na IHR ya gudanar a ranar 5 ga Yunin 2025, domin nazarin halin da ake ciki game da yaduwar cutar ta Mpox.
Humar ta kuma ce duk da cewa an samu ci gaba a wasu ƙasashe wajen fuskantar cutar, kwamitin ya gargaɗi shugaban hukumar da cewa lamarin har yanzu babbar barazana ce ga lafiyar jama’a a duniya.
Kwamitin ya danganta wannan da ci gaba da ƙaruwar yawan masu kamuwa da cutar, ciki har da ƙarin waɗanda suka kamu da cutar a yankin Yammacin Afirka, da kuma yiyuwar yaɗuwar cutar ba tare da an gano ta ba a wasu ƙasashen da ke wajen nahiyar Afirka.
Sanarwar ta ce har yanzu akwai ƙalubale wajen gudanar da aikin daƙile cutar, ciki har da matsaloli a fannin lura da yaduwar cutar da gwaje-gwaje, da kuma rashin isasshen kuɗaɗe, wanda ke hana gudanar da ayyukan dakile cutar yadda ya kamata.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ‘yansandan jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutane shida sakamakon fashewar wani abu a ƙauyen Gwabro da ke ƙaramar hukumar Tangaza na jihar.
Mai magana da yawun ‘yansanda a jihar, Ahmad Rufai ne ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce lamarin a shafi mutane da dama.
Wani ganau, Hashimu ya ce lamarin mai ban tausayi ne kuma ya faru a ranar Lahadi yayin shagalin babbar sallah.
Ya ce matasa sun kasance suna yawo daga ƙauye zuwa ƙauye domin ziyarar ‘yan uwa da dangi yayin bikin sallah.
"A yayin irin wannan yawo ne lamarin ya faru, inda bam ya fashe kuma ya hallaka wasu daga cikinsu," in ji Hashimu.
Wani hadimin shugaban karamar hukumar Tangaza, Garzali Raka, ya tabbatar da rasuwar mutanen tare da bayyana cewa an riga an yi musu jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
Wasu majiyoyi daga ƙauyen sun zargi cewa yan ta’addan Lakurawa ne suka dasa abun fashewar inda suka ce ‘yan ta’addan sun daɗe suna addabar mazauna ƙauyukan ƙaramar hukumar Tangaza da Gudu.
Sun yi kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki na gaggawa kan waɗannan ‘yan ta’addan da ke barazana ga zaman lafiya a yankunan karkara.

Asalin hoton, Getty Images
An kawo ƙarshen aikin Hajjin bana a ranar Litinin, 13 ga watan Dhul Hijjah, daidai da ranar 9 ga watan Yuni, inda Musulmi sama da miliyan 1.6 daga ƙasashe fiye da 150 suka halarci aikin hajjin na bana.
Kwamitin Aikin Hajji da Umrah na Saudiyya ne ya sanar da kammala aikin a Mina, inda aka bayyana cewa babu wata matsala da aka fuskanta.
A ranar Litinin, mataimakin sarkin yankin Makkah, Yarima Saud bin Mishaal, wanda ya bayyana haka, ya yaba wa shugabannin masarautar da suka tabbatar da ganin an gudanar da aikin hajjin lami lafiya.
Yayin da hukumomin suke tabbatar da cewa masarautar da shugabancinta na alfahari da yadda aka tafiyar da aikin hajjin cikin kwanciyar hankali da kuma nasara, sun bayyana cewa an fara shirye-shiryen Hajjin 2026 nan take.
A bana mahukuntan Saudiyya sun kafa wasu matakai da suka haɗa da abubuwan more rayuwa da tsaro da lafiya, da nufin tabbatar da cewa mahajjata sun yi aikin hajji karɓaɓɓe.

Asalin hoton, Getty Images
Rikicin siyasa na kara ta'azzara a Kamaru bayan an yi wa shugaban jam’iyyar adawa, Maurice Kamto, ɗaurin talala tun bayan dawowarsa daga ƙasar Faransa a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa kusan mambobi 60 na jam’iyyar Cameroonian Renaissance Movement (CRM) aka kama a jiya, yayin da jami’an tsaro suka hana ‘yan jam’iyyar gudanar da taro da aka shirya.
Kamto, wanda ya bayyana cewa yana cikin wani yanayi na "killacewa a gida", inda ya ce wannan mataki yana daga cikin yunƙurin hana shi bayyana ra’ayinsa da shirin takarar kujerar shugabancin ƙasa a zaben da za a gudanar a watan Oktoba mai zuwa.
Al’umma da masu fashin baƙi na siyasa a ƙasar sun nuna damuwa kan yadda ake sarrafa lamuran siyasa da kuma yadda hukumomi ke ci gaba da matsa wa ‘yan adawa lamba.