Sojojin Kamaru na fuskantar shari'a kan kashe ƙananan yara

Wasu sojoji uku da binciken gwamnatin Kamaru ya zarga da hannu wajen kashe ƙananan yara 10 da mata 3, a garin Ngarbuh cikin yankin renon Ingila, za su fara gurfana a gaban kotun soji.
Kungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Human Rights Watch dai ta yi kira ga Kamaru ta tabbatar da yin adalci a wannan shari'a da za a yi cikin birnin Yaounde.
A watan Fabrairun bana ne wasu sojoji suka harbe wasu mazauna garin Ngarbuh bayan sun zarge su da haɗa kai da 'yan fafutuka na ambazoniya.
Za dai a yi shari'ar ne ga sojoji biyu da kuma jandarma ɗaya a Younde, inda baya ga wannan laifi na kisa da ake zarginsu da aikatawa, akwai kuma wasu laifuka da ake zarginsu da aikatawa.
Ana dai zargin jami'an tsaron da laifin keta umarnin da aka basu da rusa gidaje da tayar da gobara da kuma farwa wata mata mai juna biyu.
Baya ga waɗannan dakarun tsaro, akwai kuma wasu 'yan aikin agaji goma sha bakwai da wani tsohon mai riƙe da makamai da suma ake zarginsu da hannu a wannan kisan dama ɓarnatar da dukiyoyi.
To sai dai kuma su suna zirga-zirgar ba tare da wata tsangwama ba a inda suka fake.
Akwai dai wasu manyan jami'ai sojoji waɗanda sune shugabannin sojojin da ake zargi da ba a binckesu ba ballantana a zargesu da aikata wani laifi.
Kungiyar Human Rights Watch dai ta bukaci da a tabbatar da adalci a shari'ar da za ayi, sannan kuma a bar jama'a su halarci zaman kotun.











