'Yan Najeriya suna ji a jikinsu — Sule Lamido

Lokacin karatu: Minti 1
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma ƙusa a jam'iyyar hamayya Ta Najeriya, PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce 'yan Najeriya suna ji a jikinsu salon mulkin gwamnatin Muhammadu Buhari.
A cewar sa, rikicin da ke addabar jamiyyar su ta PDP, ba wai kawai abin da ya shafe su ba ne domin a cewarsa ko ba komai 'yan Najeriya, a yanzu, suna ji a jikinsu, fiye da lokacin da PDP ke mulki.
Tsohon gwamnan na Jigawa ya yi kalaman ne a tattaunawarsu da wakilinmu a Kano Mukhtari Adamu Bawa, ku saurari yadda ta kasance.






