Ambaliya: Wasu sun koma cin beraye a India

Asalin hoton, epa
Al'ummomin wani kauye a jihar Bihar ta India sun ce babu abin da ya rage musu na abinci sai beraye, sakamakon ambaliyar ruwa da ta yanke zirga-zirga a inda gidajensu suke a kan tsibirin wani kogi.
Mutanen sun ce ba su samu wani tallafi na kayan abinci daga hukumomi ba.
Matsananciyar ambaliyar ruwa ne ci gaba da yin barna a wurare da yawa a India da Pakistan.
Koguna da yawa a arewacin India sun cika sosai, lamarin da ke da hatsari sosai.
A babban birnin Pakistan, Karachi, hadura da dama sakamakon ruwan sama sun yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane goma sha biyu tun daga ranar Alhamis.
Wasu mutanen biyar kuma sun mutu a lardin Balochistan lokacin da ambaliyar ruwa ta wuce da motocinsu.







