Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku san 'yan takarar shugaban ƙasar Kenya
A watan Agustan 2022 al'ummar ƙasar Kenya za su zabi sabon shugaban ƙasa.
Tuni ƴan takarar suka fara yaƙin neman zabe domin samun nasara.
A watan Mayun da ya gabata ma manyan ƴan takarar biyu suka zabi wadanda za su yi masu mataimaki.
Mataimakin shugaban kasar na yanzu da shi ma ke takara, ya zabi wani dan kasuwa Rigathi Gachagua yayin da tsohon firaminista Raila Odinga kuma ya zabi wata tsohuwar ministar shari'ar ƙasar Martha Karua.
Ga dai bayanai kan ƴan takarar da irin nasarorin da suka cimma a rayuwa: