Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matakan girman jariri daga farkon shigar ciki zuwa haihuwa
- Marubuci, Giulia Granchi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Daga BBC News Brésil à Sao Paulo
Alamun ciki sukan bambanta tsakanin kowace mace. Sai dai akasari ana yawan gano sabon ciki a watan farko da shigarsa, ba wai ta wata alama ba, sai dai ta jin shigar cikin, amma ana tabbatarwa ne bayan an yi gwajin ciki.
Jiki na fuskantar sauye-sauye da dama yayin samar da ɗan adam - ba za a iya lissafa su duka ba, sai dai ɗan tayi yana fara girma tun daga ɗigon maniyi zuwa jariri.
Akwai sauyi da ake samu a duk wani mataki na ciki musamman ga mahaifiya da mahaifi waɗanda a karon farko ne za su fara samun ɗa - inda za su rinƙa ƙoƙarin gano mene ne daidai mene ne ba daidai ba.
A wannan maƙala, mun zayyana yadda ciki yake a kowane mataki inda aka yi bayani kan abubuwan da ake sa ran gani idan ɗan tayi yana girma da kuma sauye-sauye da ake samu a jikin mace.
Yana da muhimmanci a tuna cewa ba lallai kowace mace ta fuskanci waɗannan alamomi ba - jikin kowa daban ne.
Abu mai muhimmanci shi ne mutum ya rinƙa tattaunawa da likitansa idan yana da wata tambaya.
Zango na farko
Watan farko (Mako na ɗaya zuwa huɗu)
A lokacin ziyarar ganin likita ta farko, abu ne da aka saba gani likitoci su yi wa mutum tambayoyi masu yawa - ciki har da tambayoyi kan kiwon lafiyar dangin mutum. Haka kuma akan yi bincike domin a gano lafiyar mahaifa da bakin mahaifa da kuma gaban mace. Kazalika za a iya yi mata gwajin kansar bakin mahaifa idan ba a taɓa yi mata ba.
Haka kuma za a yi mata gwajin fitsari a karon farko, sannan za a auna nauyinta da hawan jini da tsawo.
Ana bai wa mai juna biyu shawara ta rika shan sinadaren Vitamin da folic acid, waɗanda suke taimakawa wurin girman ɗan tayi, musamman a matakin farko na ciki. Saboda tsaro, yana da kyau mai ciki ta rinƙa bayani kan duk wani magani da take sha.
Sauyi ga mai ciki
Sinadaren da mutum ke samarwa waɗanda ake fara samu a watan farko, abu ne mai ɗumbin rikici, in ji Rodrigo Buzzini, wani likitan haihuwa da kuma darakta a Santa Joana group..
Wannan sauyin da ake samu a jikin ɗan adam zai iya jawo jiri da amai kuma mutum zai so ya keɓe kansa ba tare da ya yi wani aiki ba.
Wasu mutanen suna samun sauyi a yanayin abincin su - inda suke samun ƙarin yunwa.
Sai dai yana da muhimmanci kamar yadda likitoci suka shaida wa BBC mace mai ciki ta rinƙa cin abinci kamar yadda take ci, kamar yadda wadda ba ta da ciki take ci, haka kuma da lura da cewa jaririn zai samu abu mai kyau ko mara kyau idancaka kwatanta da yadda abubuwa suke.
Girman ɗan tayi
A wannan lokaci, jaririn yana da tsawon millimeter 0.1 zuwa 0.2. Bayan sati uku, ƙwayoyin halitta sun som gama haɗuwa kuma za a iya ganewa mace ce ko namiji duk da cewa ba zai yiwu a lokacin likita ya gane ba idan ya yi gwaji.
Shan maganin folic acid zai taimaka ƙwarai domin rage barazanar haihuwar jariri babu wasu sassa na jikinsa ko kuma matsala da ƙashin baya
Wata na biyu (Mako 5 zuwa na 8)
Idan wannan ce ziyara ta farko zuwa likita - wasu matan ba su gano juna biyu a wata na farko - akan ba su umarnin su yi gwajin da aka lissafo a can sama.
Za a kuma auna nauyi da kuma hauwan jini domin dubawa.
"A mako na shida za a iya yin sikanin, inda za a iya ganin siffar yaro a ga ci gabansa." In ji Ellen Freire wanda shi ma likitan haihuwa ne.
Sauye-sauyen da mace mai ciki take samu
Kamar yadda Freire ya bayyana, ba lallai mace ta ji wani abu ba, amma ga wasu matan, a wannan matakin ne ake samun alamu sosai na ciki.
"Tsakanin makonni biyar zuwa shida, ɗan tayin bai wuce tsawon milimita biyar ba. Wasu masu cikin suna yawan tunanin cewa ta yaya wannan dan ƙaramin sauyin zai iya yin wani tasiri? Sakamakon jikin ya shiga cikin halin juna biyu ne," kamar yadda likitan yake bayani.
Ana samun ci gaba a yadda fuskar jinjirin take da yatsu da kunnuwa, Haka kuma ƙashin baya da su ƙwaƙwalwa duk a lokacin ne suke zama halitta. Haka kuma a lokacin ne ake samun tsarin narkar da abinci haka kuma kunnuwa da idanu da hanci duk a lokacin suke samuwa.
Daga mako na shida, zuciyar ɗan tayin na fara bugawa. Za mu iya jin ƙarar bugawar zuciyar idan aka yi sikanin kuma lokaci ne na motsin rai ga iyaye. Ƙari ga abu ne na jin daɗi ga iyaye, alama ce na cewa juna biyu n mai kyau ne, kamar yadda Mista Freire ya shaida. "Amma hakan ya sha bamban da yadda kowa yake, idan aka yi la'akari da yanayin yadda jikin mutum yake da kuma tunaninsa.
Wata na uku (mako 9 zuwa 12)
Lokaci ne na komawa ofishin likita, inda a lokacin ne likitan zai saurari duk wani ƙorafi tare da amsa tambayoyi daga mace mai cikin.
"Muna tambayar hoton sikanin ɗin da aka yi na zangon farko na cikin wanda ke nuna mana muhimman abubuwa kan ɗan tayin da mahaifa, da yanayin girman an tayin wanda tuni ya ruɓanya girmansa a sikanin ɗin farko da aka yi - haka kuma ana dubawa ne a gano ko akwai barazanar wata matsala," in ji Buzzini.
Sauye-sauye ga masu ciki
Nonon mace mai ciki yana ƙara girma haka kuma kan nonon yakan yi duhu. Hakan yakan bambanta dangane dai da yadda mace take, ƙananan ƙuraje kan fito a fuska.
Yanayin cin abinci zai iya dawowa daidai.
"Cikin zai iya fara nunawa kuma abu ne mai wahala idan ba a gano cikin ba," in ji Freire.
Girman jariri
Zuwa ƙarshen wata na uku, ɗan tayin ya kai kusan centimita 10 kuma akasari nauyinsa yana kai gram 28.
Hannunsa da gaɓoɓi da yatsu da dugadugi duk sun haɗu. Kumba ta soma fitowa haka kuma haƙora za su soma haɗuwa a cikin dasashi.
Haka kuma al'aurar ɗan tayin na haɗuwa, amma duk da haka abu ne mai wahala a iya ganewa ko mace ce ko namiji idan an yi sikanin. Tsarin samar da fitsari da zagayar jini a jikin ɗan tayin duk sun soma aiki.
Zuwa wannan lokaci, ɗan tayin zai soma gane kusa da shi, inda zai soma abubua kamar buɗe ido da rufewa da baki da juya dagin hannu: " Zuwa wannan lokaci dai ya fara motsawa kuma akwai yiwuwar za a iya ganin gaɓoɓina, sai dai ya dogara ne kan idan mai sikanin ɗin zai iya hasko shi yadda ya kamata," in ji Rodrigo Buzzini.
Zango na biyu
Wata na huɗu (mako na 13 zuwa 16)
Zuwa wannan lokaci, mai ciki ta kusan kai rabi. Wannan matakin yana da muhimmanci sosai: Akwai yiwuwar sanin ko ɗan tayin mace ce ko namiji sakamakon sikanin ɗin da ake yi. Sakamakon ƙarin girman jinjiri, yiwuwar mai juna biyu ta yi ɓari ya ragu.
Sauye-sauye ga masu ciki
Zuciyar mai juna biyu za ta riƙa buga jini da sauri domin taimakon jinjirin da ita, wannan zai iya saka ta rinƙa jin jiri da kuma ɗaukewar numfashi. Haka kuma za ta iya fama da matsalar rashin zuwa bayan gida da kuma ciwon baya sakamakon ɗan tayin da ke cikinta.
Girman jariri
"Zuwa wannan lokaci, kusan dukkan sassan jikinsa sun kusa kammala haɗuwa kuma za a iya jin bugawar zuciyar ɗan tayin idan aka saka na'ura," in ji Mista Buzzini.
Gashin ido da gira da ƙumba da gashi duk za su fara fitowa. Haka kuma haƙoransa da ke cikin dasashi da kuma ƙashinsa duk sun soma ƙarfi.
A zuwa wannan lokaci, ɗan tayin zai iya soma wasu abubuwa kamar su shan yatsa da hamma da miƙa da yamutsa fuskarsa.
"Zuwa wannan lokaci, al'aurarsa ta gama haɗuwa, ya danganta da zaman ɗan tayin a cikin ciki, amma idan aka yi sikanin za a iya gane ko namiji ne ko mace. Haka kuma zuwa lokacin akwai yiwuwar ɗan tayin zai iya gane haske," in ji likitan.
Wata biyar (Mako na 17 zuwa 20)
Zuwa ƙarshen wata na biyar, likita zai sake duba mai juna biyu a karo na biyu - kuma wannan dubawar tana da muhimmanci kamar ta farkon domin duba yanayin ci gaban da ɗan tayi ke samu.
Sauye-sauye ga masu ciki
Akasarin mata sun ƙara nauyi da kilo2.5 zuwa 6.5 a wannan lokaci, haka kuma mahaifa zuwa wannan lokaci ta kai girman kankana.
Haka kuma zuwa wannan lokaci, sha'awar abinci ta ƙaru ga wasu matan haka kuma wasu matan za su iya fama da matsalar mantuwa. A wannan lokaci, mata da yawa za su rinƙa samun matsala wurin tuna abubuwa ko kuma mayar da hankali kan wannan abu.
Girman jariri
"Zuwa wannan lokaci, ɗan tayi zai iya ji a jikinsa da kuma ji da kunnensa, muna bayar da shawarar jin waƙoƙi da magana, domin bai wa ɗan tayin damar mu'amula," in ji Buzzini.
A lokacin sikanin ɗin, ƙwararru na duba sassan jiki da kuma samun bayani kan zuciya da mafitsara da ƙoda da sauran sassan jiki haka kuma likita zai ƙirga yatsun ɗan tayi domin ya tabbatar sun cika.
Wata shida (Mako na 21 zuwa 24)
"A daidai lokacin da mai ciki ta kusan kai ƙarshen zango na biyu, yana da muhimmanci a saurareta domin kada ta shiga damuwa - dakuma gaya mata cewa ciki abu ne mai kyau ga lafiyarta," in ji Ms Buzzini.
Sauye-sauye ga masu ciki
"An yi bincike kan cewa ana yawan samun hawan jini da muka matsala a maƙogwaro a wannan matakin," in ji likitan.
Haka kuma aksarin mata ana yi musu gwajin ciwon sikari.
Girman jariri
A wannan mataki, ana yin gwajin zuciyar jariri. A wannan mataki kuma, jaririn yana da nauyin sama da kilo ɗaya, kuma mahaifiyarsa na jin motsinsa sosai.
Wata bakwai (Mako na 25 zuwa 32)
A zuwa wannan lokaci, an fara tattaunawa tsakanin mai juna biyu da kuma ƙwararru kan tsarin iyali ko kuma tazarar haihuwa da kuma alamomin gargaɗi.
Sauye-sauye ga masu ciki
Ganin cewa ɗan tayi ya kai girman kusa kilo ɗaya, uwar za ta fara jin nauyin jikinta da kuma jin gajiya.
"Wani lokacin masu ciki suna cewa suna jin cikinsu yana motsawa. Ɗan tayi ne ke shaƙƙuwa, kuma ba matsala bace," in ji Rodrigo Buzzini.
Girman jariri
Zuwa wannan lokaci, ɗan tayi ya ci gaba da girma da kuma ajiye kitse a jikinsa. Ko da an haifi jinjiri lokacin haihuwarsa ba yi ba, akwai yiwuwar zai rayu bayan wata bakwai.
Zango na uku
Wata takwas (Mako na 29 zuwa 32)
Zuwa wannan lokaci, dangi za su fara ƙirga kwanakin da suka rage ga mai juna biyu ta haihu, inda ita kuma mai juna biyun za ta rinƙa zuwa awo a kai a kai - inda za a rinƙa gwada fitsarinta da nauyi da hawan jini.
Sauye-sauye ga masu ciki
Mai juna biyu za ta ci gaba da ƙara nauyi da rabin kilo a duk mako inda kuma za ta rinƙa jin wani iri idan ɗan tayin yana motsi. Sakamakon ɗan tayin zai iya kai kilo kusan biyu, akwai yiwuwar motsin da yake yi yana ƙara matsa wa awazun mai juna biyu. Za ta rinƙa shan wahala wurin gudanar da ayyukan yau da kullum.
Girman jariri
Zuwa wannan lokaci, huhu da sauran sassan jiki da ke aiki da ƙwaƙwalwa na matakin ƙarshe na haɗuwarsu haka kuma barazanar haihuwa jaririn da bai isa haihuwa babu ita.
Wata tara da wata goma (Mako na 33 zuwa 40)
Zuwa awo zai zama bayan mako biyu ko kuma mako-mako. Ciki zai shiga watansa na goma - amma bayan mako na 37, tuni jariri ya zama cikakke kuma ba a kallonsa a matsayin wanda bai isa haihuwa ba.
A wannan mataki na ƙarshe, likitoci na bayar da umarnin a yi gwaji saboda lokacin haihuwa.
Ana gudanar da gwajin jini ga mata masu rukunin jini na B streptococci, wanda shi ke jawo wata cuta mai barazana ga rayuwa a jarirai.
Idan burin mai ciki ne, likita zai iya dubawa idan za ta iya haihuwa da kanta - sai dai wannan dubawar ba wai tabbas bane - za a iya samun sauye-sauye na lokaci ko kuma ranar haihuwa jaririn.
Sauye-sauye ga masu ciki
Idan jariri ya koma wani wuri mai kyau domin haihuwa, mahaifiya za ta samu sauƙi a sassan jikinta da ke mata ciwo haka kuma za ta iya numfashi da kyau.
Girman jariri
Huhun jariri na a matakin ƙarshe na kammaluwa haka kuma ƙwaƙwalwarsa ta yi girma kuma ta shirya karɓar bayan ai daga jiki. Ana haihuwar jariri da tsawon centimita 50 haka kuma zai iya kai nauyin kilo 2.5 zuwa kilo huɗu.
Wasu labaran da za ku so karantawa