Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Najeriya na amfana da tashin farashin man fetur a duniya?
Farashin ɗanyen man na ƙara tsada a duniya sakamakon yaƙin Rasha a Ukraine.
A yanzu ana sayar da gangar mai daga dala 120 zuwa 130, sakamakon takunkumin da aka ƙaƙaba wa Rasha.
Rasha ita ce ta uku da ke samar da mai a duniya bayan Amurka da kuma Saudiyya.
Rasha na fitar da gangar danyen mai biliyan biyar a kasuwar duniya a kowace rana, kuma kusan rabin man yana tafiya ne a Turai.
Farashin mai da gas na ci gaba da tsada kuma zai ci gaba da yin tsada idan har Rasha ta dakatar da fitar da man a kasuwa.
Masana sun yi gargaɗin cewa farashin ɗanyen mai zai iya kaiwa sama da dala 300 idan har yaƙin Rasha a Ukraine ya ci gaba.
Tasirin tsadar farashin danyen mai a kasuwar duniya da yakin Rasha a Ukraine ya haddasa, shin riba ce ko hasara ga Najeriya?
Masana harakokin fetir, kamar Dr Ahmed Adamu malami a Jami'ar Nile da ke Abuja, na ganin tsadar farashin ɗanyen mai a duniya mai riba ce da kuma asara ga Najeriya.
Najeriya ita ce ƙasar da ta fi arzikin fetir a Afirka, kuma duk lokacin da farashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwar duniya Najeriya za ta kara samun kudin shiga, amma shigowa da tataccen mai zai kara tsada.
Man Rasha ya fadi kasa warwas, inda ake sayar da shi kan dala 25 yayin da kuma a kasuwar duniya ake sayar da man kan dala 128, duk ganga daya.
Ana kuma sayar da man Najeriya duk ganga kan dala 125.
Najeriya za ta iya ƙara samun kuɗin shiga amma kuma zai kasance tana kashe makudan kudi ta hanyar shigo da tattacen man fetir wanda yanzu ya yi tsada ta dalilin tsadar danyen mai a kasuwar duniya.
"Tsadar za ta fi shafar Najeriya saboda ba sayar da danyen mai take ba kai-tsaye ta karbi dala, tana bin wani tsari ne da take musayar danyen mai a ba ta tataccen man fetir."
"Idan danyen mai ya kara tsada, zai kasance kwatancin wanda Najeriya za ta karba zai kara tsada, ba wata riba da Najeriya za ta samu, ganin cewa ba kudi Nakeriya ke karba ba. sai dai ta shigo da tattacen man fetir," in ji Dr Ahmed.
Masanin ya kara da cewa yadda farashin mai ya tashi ya kamata a ce babbar riba ce ga Najeriya, amma kudin da Najeriya ke samu tana kashe su ne wajen sake shigo da tattacen mai. Hakan ya nuna duk ribar da Najeriya ta samu wurin harakar gudanar da shi take hasarar kudin.
Ko wannan zai iya haifar da tsadar fetir ga talaka?
Tuni fetir ya kara tsada a wasu kasashe sakamakon yakin Rasha a Ukraine.
Rasha na samar da kashi 5 ne kawai cikin dari na gas ga Birtaniya, kuma Amurka ba ta shigar da gas din Rasha, amma farashin ya kara tsada a Birtaniya da Amurka saboda kauracewa na Rasha da ya haifar da karancinsa a kasuwa,
Don haka masana na ganin talakawa za su iya fuskantar tsadar fetir sakamakon yakin Rasha.
Dr Ahmed ya ce nauyi zai kara yi wa gwamnatin Najeriya yawa saboda shigowa da tataccen mai zai kara mata tsada da kuma tsadar tallafin da take bayarwa.
Haka kuma yawan biyan tallafin zai rage wa gwamnati damar yin wasu abubuwa. "Idan gwamnati ta gaza dole 'yan Najeriya ne za su biya tsadar man a gidajen mai.
Yanzu Rasha ta samar da mai amma babu mai saya saboda takunkumin da kasasen yammaci suka kakaba wa Rasha, inda aka haramta wa manyan kamfanoni da ke sayen mai sayen man Rasha.
A cewar Dr Ahmed, duk lokacin da aka ce za a hukunta daya daga cikin manyan kasashen da ke samar da mai a duniya, to duka duniya ce za ta wahala
Wannan kuma babbar barazana ce ga Najeriya,
Hakan zai kara zaizaiye asusun kudaden waje na Najeriya saboda rashin samar da matattun mai a kasar da za su tace danyen mai.